Isa ga babban shafi

Masu hannu a satar Mai ne manyan makiyan Najeriya -Ahmed Lawan

Shugaban Majalisar dattawan Najeriya, Ahmed Lawan ya bayyana kungiyoyi da masu hannu wajen satar man kasar a matsayin manyan makiyan kasar baki daya.

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan a ofishinsa dake Majalisar.
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan a ofishinsa dake Majalisar. © Ahmad Lawan Twitter
Talla

Ahmed Lawan ya ce a halin yanzu Najeriya na asarar tsakanin ganga dubu 700 zuwa ganga dubu 900 kowacce rana sakamakon tsanantar satar man da ake yi, wanda adadin sa ya kai kashi 35 na kudaden shigar da kasar ke samu.

Shugaban Majalisar ya bayyana cewar wadannan sata ya dauki wani sabon salo ganin yadda barayin suka kaddamar da yaki akan kasa, saboda haka ya dace a dauki mataki mai tsauri akansu.

Lawan wanda ya ke wannan jawabi lokacin da majalisdar ta karbi shugaban kasa Muhammadu Buhari domin gabatar da kasafin kudin shekara mai zuwa, ya yaba da yadda shugaban ya kawo kasafin kudin cikin lokaci, wanda zai bai wa 'yan majalisun damar tantance shi da kuma amincewa cikin lokaci.

Shugaban majalisar ya bukaci ganin kasafin kudin ya mayar da hankali akan shirin kammala manyan ayyukan da ake gudanarwa a sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.