Isa ga babban shafi

Kin baiwa kudancin Najeriya shugabancin PDP zai haifar da rigima - Wike

Gwamnan jihar Rivers dake Najeriya, Nyesome Wike ya sanar da cewar ya amince da Atiku Abubakar wanda ya kada shi a zaben fidda gwanin da Jam’iyyar su ta PDP ta shirya a matsayin dan takarar zaben shugaban kasa, amma kuma yace har yanzu yana kan matsayinsa cewar dole sai shugaban Jam’iyyar Iyiorchia Ayu ya sauka daga mukaminsa.

Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike
Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike Daily Trsut
Talla

Wike ya bayyana haka ne a sakon da ya aikewa Atiku bayan ganawar da yayi da tawagar da ya sake tura masa domin sasanta rikicin dake tsakanin su, wanda ya kaiga Jam’iyyar ta dakatar da yakin neman zaben da ta fara domin magance matsalar.

Gwamnan da magoya bayansa da suka hada da wasu gwamnonin jihohi guda 5 da wasu fitattun yayan Jam’iyyar PDP sun ki shiga tawagar yakin neman zaben Atiku saboda abinda suka kira rashin adalci wajen raba mukamai, ganin yadda shugaban Jam’iyyar da dan takarar shugaban kasa suka fito daga yankin arewacin kasar.

Wike ya zargi wasu mutane da ya kira a matsayin masu amfana da jam’iyyar da rura wutar rikicin saboda amfana da suke yi, yayin da yace babu wani mahaluki da zai sa shi sauya matsayin sa na ganin shugabancin Jam’iyyar ya koma kudancin Najeriya.

Gwamnan yace muddin aka hana yankin kudancin Najeriya shugabancin Jam’iyyar to rikici na nan kwance, domin kuwa Ayu da kansa ya jaddada haka kafin gudanar da zaben fidda gwani wanda yanzu yake musantawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.