Isa ga babban shafi

Najeriya ta sha alwashin bin matakan da suka dace don ci gaba da shari'ar Nnamdi Kanu

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewar za ta bi matakan da suka dace wajen ci gaba da shari’ar da ake yi wa Nnamdi Kanu bayan kotun daukaka kara ta yi watsi da tuhume-tuhumen da ake masa sakamakon laifin dauko shi daga kasar Kenya ba bisa ka’ida ba.

Jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu.
Jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu. AFP - STEFAN HEUNIS
Talla

Ministan shari’a Abubakar Malami ya ce hukuncin kotun kolin ya nuna sakin Kanu ne amma ba sallamarsa daga karar da ake yi akansa ba, saboda haka har yanzu tuhume-tuhumen da ake masa na cin amanar kasa suna nan.

Malami ta hannun mai taimaka masa a bangaren yada labarai Umar Gwandu ya ce har yanzu wadancan kararraki da aka shigar akan Kanu kafin ya tsallake belin da aka bashi ya gudu suna nan a gaban shari’a.

Ministan ya ce kuma za suyi nazari akan hukuncin kotun na jiya domin daukar matakan da suka dace.

Kotun daukaka kara a Najeriya ta yanke hukuncin watsi da karar da aka shigar a gaban ta na cin amanar kasa saboda abinda ta kira kin bin ka’ida wajen dauko Kanu daga Kenya bayan ya gudu daga Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.