Isa ga babban shafi

Hukumar DSS ta bukaci kwantar da hankula bayan gargadin Amurka da Birtaniya

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya DSS ta bukaci ‘yan kasar da su kwantar da hankalinsu, dangane da wani rahoton ofisoshin Jakadancin Amurka, da Birtaniya da kuma Italiya da ke Najeriyar, wanda a cikinsa suka ce, akwai fargabar kai harin ta’addanci a sassan birnin Abuja.

Jami'an DSS a Najeriya.
Jami'an DSS a Najeriya. guardian.ng
Talla

Ofisoshin Jakadancin kasashen sun gargadi mutanen su da kasance masu taka tsan-tsan yayin tafiyar da harkokinsu nay au da kullum a babban birnin Najeriyar.

Kakakin hukumar Peter Afunanya ya ce DSS ta samu shawarwari dangane da al’amuran tsaro daga ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja, kuma suna daukar matakan da suka dace don baiwa jama'a kariya.

A cewar hukumar babu bukatar firgici da shiga tashin hankali game da gargadin na Amurka da Birtaniya, dai dai lokacin da hukumomin tsaron kasar ke aiki tukuru wajen kakkabe duk wata barazanar tsaro.

A lahadin da ta ne ofisoshin jakadancin Amurka da Birtaniya da ke Najeriya, a cikin maban-bantan sanarwar da suka fitar, suka gargadi al'ummomin kasashen su game da yuwuwar fuskantar hare-haren ta’addanci a birnin Abuja da wasu biranen kasar.

Sai dai hukumar DSS ta ce tuni take daukar matakan da suka dace wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.