Isa ga babban shafi

Jami'an DSS sun kama kwamandan ISWAP da ya shirya harin bam din Okene

Hukumar tsaron Najeriya ta DSS ta sanar da kama babban kwamandan kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP AbdulMumin Otaru wanda ake kira da Abu Mikdad.

'Yan sandan Najeriya na hukumar tsaron farin kaya ta DSS.
'Yan sandan Najeriya na hukumar tsaron farin kaya ta DSS. AP - Sunday Alamba
Talla

Binciken jami’an tsaron dai ya nuna cewar Abu Mikdad din ake zargi da shirya harin harin bam din da aka kai kan fadar Sarkin Okene ‘Ohinoyi na Ebiraland’ da ke jihar Kogi.

Mutane hudu suka mutu a harin, wanda ya faru a karshen watan Disamba, lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar domin kaddamar da wasu ayyuka da Gwamna Yahaya Bello ya aiwatar.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Peter Afunanya kakakin hukumar ta DSS ya ce kwamandan na ISWAP ya samu rauni a kafarsa ta hagu yayin da yake kokarin tserewa samamen da suka kai maboyarsa.

Afunanya ya kara da cewa kwamandan na ISWAP da suka kama yana da hannu a harin da aka kai kan gidan yarin Kuje a Abuja, ranar 5 ga Yuli a 2022; da kuma harin da ‘yan ta’adda suka kai a garin Ajaokuta, a ranar 5 ga Agusta, a 2022, inda aka yi garkuwa da wasu 'yan kasar India uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.