Isa ga babban shafi

Iyayen daliban kwalejin Yauri sun fara sayar da gonaki don karbo yaransu daga hannun 'yan bindiga

A Najeriya Iyayen daliban kwalejin tarayya ta Yauri da ke jihar Kebbi a arewacin kasar sun fara sayar da gonakin da sauran dukkanin abubuwan da suka mallaka don tattara kudin da yawansu ya kai Naira miliyan 100 don karbo ‘ya’yansu mata da ke hannun ‘yan bindigar daji fiye da watanni 20 da suka gabata.

Wasu daga cikin daliban Islamiyar Salihu Tanko dake Tegina yayin ganawa da gwamnan Neja bayan kubutar da su daga hannun 'yan bindiga inda suka kwashe sama da kwanaki 88. 27/08/21.
Wasu daga cikin daliban Islamiyar Salihu Tanko dake Tegina yayin ganawa da gwamnan Neja bayan kubutar da su daga hannun 'yan bindiga inda suka kwashe sama da kwanaki 88. 27/08/21. AP - AP Photo
Talla

Tun a shekarar 2021 ne ‘yan matan da shekarunsu bai gaza 12 zuwa 16 ba suke tsare a hannun ‘yan bindigar wadanda suka farmaki makarantarsu ta kwana da ke jihar Kebbi tare da sace su, ko da ya ke an saki kaso mai yawa amma ‘yammatan su 11 suke ci gaba da kasancewa a hannunsu.

‘Yan bindigar dai sun bukaci biyansu fansar miliyan 100 gabanin sakin ‘yammatan su 11 yayinda iyayen suka gaza samun taimako daga mahukuntan jihar da na tarayya baki daya cikin fiye da watanni 20 da suka shafe a hannun ‘yan bindigar.

Akwai dai bayanan da ke cewa, ‘yan bindigar sun auri kusan dukkanin yaran 11 yayinda wasu daga cikinsu tuni suka haifi ‘ya’ya.

A wani jawabinsa yayin taron manema labarai da ya kira game da halin da yaran ke ciki da kuma kokarin karbo su daga hannun ‘yan bindigar, Salim Kaoje shugaban kwalejin ya bukaci dauki daga daidaikun jama’a don ganin an ceto yaran.

A cewar Kaoje basu da zabin da ya wuce neman agaji daga jama’a da kuma sayar da ddukkanin kadarorin da suka mallaka don ceto rayuwar yaran wadanda aka sace a ranar 17 ga watan Yunin shekarar 2021, bayan gaza samun agaji daga gwamnati don shiga tsakani da ‘yan bindigar da nufin kubutar da yaran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.