Isa ga babban shafi

Najeriya ce ta 11 a jerin kasashen da ke tilastawa Mata aure da karancin shekaru

Kiraye-kiraye na ci gaba da tsananta ga mahukuntan Najeriya game da daukar matakan gaggawa wajen haramta auren wuri da ke ci gama da zama babbar illa ga rayuwar tarin Mata a sassan kasar.

India ke sahun kasashe 'yan gaba gaba da ke aurar da kananan yara.
India ke sahun kasashe 'yan gaba gaba da ke aurar da kananan yara. AFP - GABRIEL BOUYS
Talla

Wasu jaridun kasar sun ruwaito cewa, yanzu haka an shigar da takardun korafi kusan dubu 500 ga Ofishin shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari don ganin ya samar da dokar da za ta haramta auran wurin musamman ga mazauna karkara.

Wasu alkaluma da jaridar Punch ta tattara sun nuna cewa zuwa yanzu akwai korafe-korafe akalla dubu 473 da 429 game da bukatar daukar matakin haramta auren na wuri a Najeriya ciki kuwa har da wata mafi jan hankali da guda cikin kungiyoyin fararen hular kasar ta shigar.

Koken wanda aka yiwa lakabi da ‘‘Ba laifinki ba ne’’ ya bukaci gwamnatin Najeriya ta yi amfani da dokokin kundin tsarin mulkin kasar da aka yiwa gyaran fuska a 1999 wanda cikinsa dokoki ko kuma hakkokin yara ya haramta yi musu auren wuri.

Takardar koken ga shugaba Muhammadu Buhari ta yi tuni game da dokar 2003 da ta haramta yiwa yara aure idan basu kai shekaru 18 a duniya.

Wannan koke dai na zuwa ne a dai dai lokacin da wani rahoton UNICEF na baya-bayan nan ke bayyana Najeriya a matsayin ta 11 cikin kasashen da ke yiwa yara auren wuri.

Rahoton na UNICEF ya bayyana cewa kashi 44 cikin dari na matan Najeriya na fuskantar auren wuri ta yadda ake kaisu dakin miji tun gabanin cika shekaru 18 a Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.