Isa ga babban shafi

Gwamnan Jigawa ya amince da nadin Muhammad Hameem Nuhu Sanusi a matsayin sabon Sarkin Dutse

Gwamnan JIhar Jigawa dake Najeriya Badaru Abubakar ya amice da nadin Muhammad Hameem Nuhu Sanusi a matsayin sabon Sarkin Dutse, domin maye gurbin mahaifinsa wanda ya rasu a makon jiya. 

Gwamnan Jigawa Muhammad Badaru Abubakar
Gwamnan Jigawa Muhammad Badaru Abubakar Daily Trust
Talla

Wannan ya biyo bayan shawarar da masu zaben sarki daga Masarautar Dutse suka gabatar, wadan ya amince da nadin Hameem ba tare da wata hammaya ba. 

Wata sanarwa daga Majalisar Sarki tace an gabatar da sunan Hameem tare da wasu ‘yayan sarki biyu, amma sai aka zabe shi domin maye gurbin mahaifinsa. 

Sanarwar tace daga yau 5 ga watan Fabarairu, gwamna Abubakar ya amince da Muhammad hammen Nuhu Sanusi a matsayin sabon Sarkin Dutse. 

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tururuwa zuwa garin Dutse domin gabatar da ta’aziyar rasuwar Sarki Sanusi wanda akasarin jama’a ke jinjina masa saboda adalcinsa da jajircewa da kuma taimakon jama’a lokacin da yake rike da Masarautar. 

Dubban mutane ne suka halarci jana’izarsa da akayi a garin Dutse bayan rasuwar da Allah ya masa a wani asibiti dake Abuja.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.