Isa ga babban shafi

Zaben Najeriya cikin alkaluma a takaice

Najeriya na daga cikin kasashen da zabukanta ke daukar hankalin duniya la’akari da tasirin kasar a ciki da wajen nahiyar Afirka a fannoni daban daban, ciki kuwa har da tattalin arziki da tsaro.

Takardun kada kuri'a a Najeriya
Takardun kada kuri'a a Najeriya © Amélie Tulet / RFI
Talla

‘Yan takara 18 ne dai suke karawa da juna a kan kujerar shugabancin kasar, wadda ita ce mafi karfin tattalin arziki a Afirka. A dai ranar ta 25 ga watan Fabarairu ce kuma ake zaben ‘yan majalisun dokokin Najeriyar da suka kunshi ‘yan majalisar dattijai 109, da na wakilai 360.

‘Yan takarar da masu sharhi ke kallon su ke kan gaba a zaben shugabancin Najeriyar sun hada da Atiku Abubakar, Bola Ahmad Tinubu da kuma Peter Obi.

Atiku Abubakar

Atiku Abubakar mai shekaru 76 na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, tsohon mataimakin shugaban Najeriya ne a zamanin gwamnatin tsohon shugaba Janar Olusegun Obasanjo mai ritaya daga 1999 zuwa 2007.

Dan takarar Jam'iyyar PDP,  Atiku Abubakar yayin kada kuri'arsa a Yola da ke Adamawa.
Dan takarar Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar yayin kada kuri'arsa a Yola da ke Adamawa. AP - Sunday Alamba

Sau shida Atiku Abubakar ya nemi darewa kujerar mulkin Najeriya, inda ya samu nasarar lashe zaben fidda gwani sau uku a shekarun 2007, 2019 da kuma 2023 da a yanzu yake takara karkashin jam’iyyyar PDP.

Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya rasa zabukan fidda gwanin neman takarar shugabancin Najeriyar ne kuma a shekarun 1993, 2011 da kuma 2015.

Bola Tinubu

Bola Ahhmad Tinubu mai shekaru 70 na jam’iyyyar APC mai mulkin Najeriya, tsohon gwamnan jihar Lagos ne kan wa’adi biyu a tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007.

Lokacin da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya halarci rumfar zabensa a Lagos (2023/02/25)
Lokacin da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya halarci rumfar zabensa a Lagos (2023/02/25) AP - Ben Curtis

Dan takarar ya taba wakiltar yammacin jihar Legas a majalisar dattijai a zamanin mulkin Jamhuriyya ta uku.

Peter Obi

Peter Obi mai shekaru 61 na jam'iyyar Labour. Tsohon Gwamnan jihar Anambra ne da ke kudu maso gabashin Najeriya har sau biyu, yana da farin jini sosai a tsakanin matasa masu kada kuri’a musamman a kudancin kasar.

Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour ke kada kuri'arsa a Anambra. 2023/02/25
Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour ke kada kuri'arsa a Anambra. 2023/02/25 AP - Mosa'ab Elshamy

Magoya bayansa da ke kiran Kansu da "OBIdients" sun shahara sosai a shafukan sada zumunta, inda suke bayyana cewa shi ne dan takara daya tilo da zai iya inganta tattalin arzikin Najeriya.

Adadin ‘yan Najeriya da suka cancanci kada kuri’a

Alkaluman da hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta fitar sun nuna cewar, mutane fiye da miliyan 87 ne suka mallaki katin zabe na dindindin.

Yadda wasu masu kada kuri'a ke neman sunayensu gabanin bude rumfunan zabe a Lagos. 2023/02/25.
Yadda wasu masu kada kuri'a ke neman sunayensu gabanin bude rumfunan zabe a Lagos. 2023/02/25. AP - Mosa'ab Elshamy

Jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya ke kan gaba wajen yawan wadanda suka cancaci jefa kuri’a da adadin mutane miliyan 7.6 da suka yi rajista.

Jihar Ekiti kuwa, da itama take a yankin kudu maso yammacin Najeriya, ita ce ta fi kowacce jiha karancin masu kada kuri’a, da adadin mutane 987,647.

Adadin ma’aikatan da hukumar INEC ke bukata

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta ce ta na bukatar adadin jami’an da yawansu ya kai miliyan 1 da dubu 265 da 227 jimilla.

Wani jami'in zabe na amfani da na'urar BVAS domin tantance wani mutun da ke shirin kada kuri'arsa. 2023/02/25.
Wani jami'in zabe na amfani da na'urar BVAS domin tantance wani mutun da ke shirin kada kuri'arsa. 2023/02/25. AP - Mosa'ab Elshamy

Daga cikin adadin INEC ta ce tana bukatar baturan zabe da mataimakansu dubu 707 da 384, sai jami’ab da ke sa idanu kan ayyukan zabe dubu 17 da 685, da jami’an tsaro dubu 530 da 538 da za su sa ido a zaben.

Rabe-raben wadanda suka cancanci zabe a Najeriya

Daga cikin adadin wadanda suka cancanci kada kuri'a, kashi 52.5 cikin 100 ​​maza ne, kwatankwacin mutane miliyan 49, da dubu 54 da 162.

Mata masu jefa kuri'a kuwa kashi 47.5 cikin 100, kwatankwacin mutane miliyan 44 da dubu 414 da 846.

Adadin rumfunan zabe a Najeriya

Za a gudanar da zabe a rumfuna dubu 176 da 606 da ke yankuna ko mazabu dubu 8 da 809, wadanda suke a kananan hukumomi 774 a fadin kasar.

Sai dai ba za a gudanar da zabe a rumfuna 240 ba, saboda ko dai dalilai na rashin tsaro ko kuma saboda rasa muhallai da dubban mutane suka yi a dalilin tashin hankalin da aka samu a yankunan.

Dokar zabe kan wa'adin bayyana sakamako

A karkashin dokar zaben Najeriya da ka yi wa kwaskwarima a shekarar 2022, shugaban hukumar INEC na da wa’adin kwanaki 14 ne daga ranar da aka kada kuri’a domin tabbatar da sakamakon karshe na zaben shugaban kasa.

Sharuddan zama shugaban Najeriya

Baya ga lashe mafi rinjayen yawan kuri’un da aka jefa, dole ne dan takara ya lashe akalla kashi 25 cikin 100 a tsakanin kashi 2 bisa 3 (2/3) na kuri’un da aka kada a jihohin Najeriya da kuma babban birnin kasar Abuja.

Zagaye na biyu

Idan har dukkanin ‘yan takarar da suka fafata suka gaza cika sharuddan lashe zaben kujerar shugaban kasa da muka bayyana, to fa ya zama tilas a sake gudanar da zaben zagaye na biyu, inda za a kara a tsakanin ‘yan takara biyu da suka fi yawan kuri’u a zagayen farko.

Yana da kyau mai karatu ya sani cewa, ba a taba samun lokacin da aka kai zagaye na biyu a zaben Najeriya ba. Kamar yadda tarihi ya nuna, dukkanin zabukan kasar na shugaban kasa sun kammala ne a zubin farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.