Isa ga babban shafi

Zaben Najeriya: An samu fitowar masu zabe da dama a Sokoto

Rahotanni daga Najeriya na cewa, an samu fitowar dimbin masu kada kuri’a a jihar Sokoto da ke Arewacin kasar, domin gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.

Yadda masu zabe ke kada kuri'a a arewacin Najeriya
Yadda masu zabe ke kada kuri'a a arewacin Najeriya © dailytrust
Talla

Rumfunan zafe da dama ssun samu halartar masu kada kuri’a, yayin da jama’a ke kokariun zabar wanda zai maye gurbin shugaba mai ci Muhammadu Buhari.

An kuma lura cewa zaben na gudana cikin kwanciyar hankali ya zuwa yanzu.

Bayanai na cewa, an fara kada kuri'a tsakanin karfe 8:30 na safe a rumfunan zabe da dama.

Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa wata na’ura mai suna Bimodal Voter Accreditation System (BVAS), it ace ke bawa jami’an INEC matsala wajen tantance masu kada kuri’a.

An kuma lura da cewa ayarin motocin Sojoji dauke da manyan makamai na sintiri a cikin birnin Sokoto da kewaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.