Isa ga babban shafi

Bola Tinubu na jam'iyyar APC ya lashe zaben shugaban kasa a Najeriya

Hukumar zabe a Najeriya INEC ta sanar da sunan Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara lashe zaben shugabancin kasar da aka yi ranar asabar din da ta gabata.

Sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.
Sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu. © daily trust
Talla

Tinubu dan takarar jam’iyya mai mulki ya doke ‘yan takarar shugabancin kasa 17 da suka fafata da shi daga mabanbantan jam’iyyu a babban zaben na Najeriya.

Alkaluman da INEC ta tattara na nuna cewa Tinubu ya samu fiye da kashi 25 na kauri’un da aka kada a jihohin Najeriya 30 cikin 36 da kasar ke da su.

Shugaban hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu da ke bayar da sanarwar alkaluman zaben ya ce Bola Ahmed Tinubu ya samu kuri’un ya yawansu ya kai miliyan 8 da dubu 794 da 726.

Alkaluman INEC sun bayyana Alhaji Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP a matsayin na biyu da yawan kuri’u miliyan 6 da dubu 984 da 520 yayinda Peter Obi na jam’iyyar Labour ya zaman a 3 da yawan miliyan 6 da dubu 101 da 533 yayinda Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar NNPP ya zo na 4 da yawan kuri’u miliyan 1 da 496 da 687.

Majiyoyin INEC sun bayyana cewa da tsakar ranar yau ne hukumar za ta mikawa Bola Tinubu takardar shaidar lashe zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.