Isa ga babban shafi

Tinubu ya bukaci magoya bayansa da ke Legas su kwantar da hankula

‘Dan takarar shugabancin Najeriya karkashin inuwar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci magoya bayansa a jihar Lagos da su kwantar da hankulansu da kuma kaucewa tashin hankali, sakamakon nasarar da Peter Obi na Jam’iyyar Labour ya samu. 

Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed Tinubu © daily trust
Talla

Wata sanarwar da daraktan yada labarai na yakin neman zabensa Bayo Onanuga ya fitar, tace bai dace sakamakon zaben Lagos da Jam’iyyar Labour ta samu ya tada hankalin jama’a ba wajen yin tarzoma, inda ya kara da cewar dama abin da dimokiradiya ta gada kenan wajen bawa jama’a damar zabin abinda suke so. 

Tinubu yace a matsayinsa na wanda ya fahimci dimokiradiya, ya zame masa wajibi ya amince da sakamakon zabe duk yadda ya kaya koda bai gamsar da shi ba. 

Sanarwar tace Tinubu ya bayyana bakin cikinsa da rahotan samun tashi hankali a wasu sassan Lagos, musamman harin da ake rade radin an kai kan ‘yan kabilar Igbo, inda nan take yayi Allah wadai da shi. 

‘Dan takaran APCn yace rashin nasarar jam’iyyarsa a Lagos ba lasisi ne na tashin hankali ba, domin shima zai samu nasara a wasu jihohi wadanda ba nasa ba, saboda haka yana da muhimmaci mutane su tabbatar da zaman lafiya a kasa baki daya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.