Isa ga babban shafi

INEC za ta mika sakamakon lashe zabe ga Tinubu kowanne lokaci daga yanzu

Shugaban hukumar zaben Najeriya INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya sanar da karfe 3 na tsakar ranar yau laraba a matsayin lokacin da zai mika sakamakon lashe zaben shugaban kasa ga Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima.

Shugaban hukumar Zabe Farfesa Mahmood Yakubu yayin sanar da sanar da sakamakon zaben shugaban kasa a Abuja.
Shugaban hukumar Zabe Farfesa Mahmood Yakubu yayin sanar da sanar da sakamakon zaben shugaban kasa a Abuja. AP - Ben Curtis
Talla

Nasarar Bola Tinubu a zaben na Najeriya na zuwa ne bayan lashe fiye da kashi 25 na kuri’un da aka kada a jihohin Najeriya 30 yayin zaben ranar 25 ga watan Fabarairu.

Jerin jihohin da Tinubu ya lashe a zaben shugaban kasar sun hada da jihar Rivers da Borno da Jigawa da Zamfara da Benueda jihar Kogi baya ga Kwara da Neja da kuma Osun kana Ekiti da Ondo da Oyo da jihar Ogun.

A bangare guda Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP ya lashe zaben jihohin Katsina da Kebbi da Sokoto da Jihar Kaduna baya ga Gombe da Yobe da Bauchi da kuma Adamawa kana Taraba.

Sauran jihohin da ya lashe zaben sun hada da Osun, da Akwa Ibom da kuma Bayelsa.

A bangare guda Peter Obi ya lashe jihohin Edo da Cross River da Delta da Lagos da Abuja fadar gwamnatin kasat kana Pulato da Imo da Ebonyi da Nasarawa da Anambra da Abia da kuma Enugu.

A bangare guda Rabi’u Kwankwaso na jam’iyyar NNPP ya lashe jihar Kano ne kadai ko da ya ke ya samu kuri’u a wasu jihohin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.