Isa ga babban shafi

Sabbin fuskokin da za su mamaye sabuwar Majalisar dattawan Najeriya ta 10

Sakamakon zaben majalisar dattawan Najeriya da aka gudanar a karshe mako, ya nuna yadda za a samu sabbin fuskoki a zauren majalisar ta 10 da za a kafa karkashin sabuwar gwamnatin da Bola Ahmed Tinubu zai jagoranta. 

Zauren Majalisar Dattawan Najeriya.
Zauren Majalisar Dattawan Najeriya. © Premiumtimes
Talla

Daga cikin sabbin sanatocin da aka zaba akwai Kawu Sumaila daga jihar Kano, wanda ya lashe zabe a karkashin inuwar jam’iyar NNPP. 

A Kaduna kuwa, dukkanin sanatoci uku da za su wakilci jihar sabbi ne daga jam’iyar PDP, inda Barrister Khalid Ibrahim zai wakilci yankin Arewacin jihar, sai Lawal Adamu a Kaduna ta tsakiya kana Barrister Sunday Marshal Katung a kudancin Kaduna. 

A jihar Zamfara, tsohon gwamnan Abdulaziz Yari ne ya lashe zaben kujerar sanatan da ke wakiltar Zamfara ta yamma a karkashin inuwar jam’iyar APC, yayinda tsohon gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo ya lashe kujerar sanatan da ke wakiltar Gombe ta Arewa. 

Gwamna Abubakar Sani Bello na Neja shi ma zai samu lekawa zauren majalisar dattawa ta 10 don ya wakilci yankin Neja ta Arewa. 

A jihar Nasarawa, Ahmed Wadada na jam’iyar SDP ne ya lashe kujerar sanatan da ke wakiltar Nasarawa ta yamma a majalisar dattawa, sai kuma Mohammed Onawo na jam’iyar PDP da ya kada tsohon gwamnan jihar Tanko Al-Makura don ya wakilci Nasarawa ta Kudu. 

Shi kuwa kakakin majalisar dokokin jihar Akwa Ibom Anieken Bassey ya lashe kujerar sanatan da ke wakiltar yankin Arewa maso gabashin Akwa Ibom a karkashin inuwar jam’iyar PDP. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.