Najeriya: 'Yan bindiga sun kashe wani basarake a Kano
An bindige mai unguwar kauyen Maigari a karamar hukumar Rimin Gado ta jihar Kano a Najeriya, Dahiru Abba har lahira.
Wallafawa ranar:
Dansa, wanda shine shugaban karamar hukumar ta Rimin Gadon, Barrister Munir Dahiru Maigari, ne ya tabbbatar da aukuwa lamarin ga jaridar ‘Daily Trust’ da ake wallafawa a Najeriya.
Ya ce lamarin ya auku ne da misalign karfe 2 na dare, kuma har an yi masa jana’iza da safiyar Lahadin nan.
Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun kutsa gidan basaraken da karfin tuwo, inda suka ci mutuncinsa kafin su bude masa wuta.
Da aka tuntube shi, kakakin rundunar ‘yan sandan ljihar Kano, SP Abdulllahi Haruna Kiyawa ya ce ba shi da masaniya a game da lamarin, amma zai bincika.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu