Isa ga babban shafi

Najeriya: INEC ta cire sunan Doguwa daga wadanda suka lashe zabe

Hukumar zabe a Najeriya ta cire sunan shugaban masu rinjaye na majlisar wakilan kasar Alhassan Ado Doguwa daga jerin sunayen wadanda suka lashe zaben da ya gudan a wataan da ya gabata.

Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zaben Najeriya.
Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zaben Najeriya. AP
Talla

Hukumar zaben ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Doguwa/Tudun-Wada ta jihar Kano.

Tun da farko babban baturen zabe na jihar Kano, Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai ya sanar da Doguwa na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Doguwa da Tudun-Wada da kuri’u dubu  39,732, inda ya doke abokin hamayyarsa, na jam’iyyar  NNPP Yushau Salisu Abdullahi, wanda ya samu kuri’u  34,798.

Sai dai a sabon jerin sunayen da aka fitar na ‘yan majlisar dokokin Tarayyar, babu suna Alhassan Ado Doguwa.

A wani bidiyo da ya karade shafukan intanet, ana iya ganin farfesan da yake  bayyana sakamakon zaben a tsorace, jiki na rawa a lokacin da yake karanta sakamakon zaben ‘yan majalisar wakilai  na mazabar Doguwa da Tudun-Wada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.