Isa ga babban shafi

Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta yi watsi da nasarar da Tinubu ya samu

Kungiyar siyasa ta Yarabawa a Najeriya, da ake kira Afenifere, ta yi watsi da nasarar Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa, inda ta ce Peter Obi shi ne halastaccen zababben shugaba.

Dan takarar jam'iyyar Labour daga hagu kenan, Peter Obi lokacin da yake gaisawa da zababben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, A wajen taron zaman lafiya da ya gudana a Abuja, gabanin babban zaben kasar.
Dan takarar jam'iyyar Labour daga hagu kenan, Peter Obi lokacin da yake gaisawa da zababben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, A wajen taron zaman lafiya da ya gudana a Abuja, gabanin babban zaben kasar. AP - Bayo Omoboriowo
Talla

Kungiyar ta ce zaben da aka gudanar na ranar 25 ga watan Fabrairu, ya tabbatar da cewa jam’iyyar Labour ce ta samu nasara.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwar bayan babban taron kungiyar da aka gudanar a Isanya-Ogbo da ke karamar hukumar Ijebu-Ode a jihar Ogun.

Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na kasa Pa Ayo Adebanjo, ta ce shakka babu an tafka magudi a zaben da ya gudana na zzaben shugabancin Najeriyar.

Haka zalika, Afenifere ta musanta labarin da ke cewa ta aike da sakon taya murna ga zababben shugaban Najeriyar, Bola Ahmed Tinubu.

A ranar Juma’ar da ta wuce ne, babban sakataren kungiyar na kasa, Jare Ajayi, ya aike da sakon taya murna ga zababben shugaban Najweriyar, tare da kira ga wadanda basu amince da ssakamakon zaben ba, da su garzaya kotu.

Yanzu haka dai, Afenifere ta cet ana goyon bayan Peter Obi na jam’iyyar Labour, game da kalubalantar sakamakon zaben da ya ce zai yi a gaban kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.