Isa ga babban shafi
Hattara jama'a!

‘Yan damfara sun bude shafin RFI Hausa na bogi a Facebook

Wasu kwararrun 'yan damfara sun bude shafin bogi na RFI  Hausa, inda suke neman al’umma su zuba kudadensu a wata sana’ar da suka yi ikirarin cewa  ana samun riba da ta ninka uwar kudin da aka zuba.

Masoya RFI Hausa ku yi hattara da 'yan damfarar da ke fakewa da sunan RFI Hausa suna cutar jama'a.
Masoya RFI Hausa ku yi hattara da 'yan damfarar da ke fakewa da sunan RFI Hausa suna cutar jama'a. REUTERS/Kacper Pempel/Illustration
Talla

 

RFI Hausa na amfani da wannan dama don ankarar da masu bibiyar ta cewa ba za ta taba tallata wani abu makamancin haka a shafukanta na dandalin sada zumunta ba, hasali ma ba za ta nemI wani ya aiko mata da kudi ba. 

Ya kamata jama'a su gane cewa, babu wata sana’a ta gaskiya da za ta bada ribar da ta ninka uwar kudi a cikin ‘yan mintuna, saboda haka a yi hattara. 

Sashen Hausa na RFI na yi wa wadannan ‘yan damfara da suka bude shafinta na bogi kashedin cewa, akwai yiwuwar daukar mataki na shari’a a kansu idan aka gano su. 

Koda yake jim kadan bayan asirinsu ya fara tonuwa, 'yan damfarar sun goge wannan shafin na bogi da suka bude.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.