Isa ga babban shafi

Ma'aikatan INEC a Bauchi sun yi zanga-zanga kan rashin biyansu kudin alawus

Wasu jami’an wucin-gadi na hukumar zaben Najeriya a jihar Bauchi sun gudanar da zanga-zanga don nuna rashin jin dadinsu a game da kudin alawus na sufuri dinsu da hukumar ta rike tun bayan aikin da suka yi mata a watan da ya gabata.

Wasu daa cikin ma'aikatan hukumar zaben Najeriya dauke da kayayyakin zabe.
Wasu daa cikin ma'aikatan hukumar zaben Najeriya dauke da kayayyakin zabe. AFP/Pius Utomi Ekpei
Talla

Wannan lamari ne ma ya janyo tsaiko wajen rarraba kayayyakin zabe a karamar hukumar Bauchi ta jihar, saboda duk kuwa da wadannan ma’aikata sun karbi kayayyakin zabe, sun ki barin shelkwatar hukumar.

Amma biyo bayan shiga tsakani da wasu manyan jami’an INEC suka yi ne aka biya ma’aikatan inda suka bar harabar shelkwatar da misalin karfe 9 da mintuna 12 ta safiyar Asabar  din nan.

Wannan matsala ta tsaiko a wajen biyan ma’aikatan wucin-gadi da suka yi wa hukumar zabe ta zama ruwan dare, da dama a sassa dabam dabam ke korafi a kan haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.