Isa ga babban shafi

Sharhin wasu jaridu a kan zaben gwamnoni a Najeriya

Zaben gwamnonin da na 'yan majalisun dokokinsu ya kankama a Najeriya inda miliyoyin 'yan kasar suka sake fita domin kada kuri'unsu a jihohi 28.

Wasu 'yan Najeriya yayin duba wasu jaridu da ake wallafa wa a kasar domin samun bayanai.
Wasu 'yan Najeriya yayin duba wasu jaridu da ake wallafa wa a kasar domin samun bayanai. AP - Sunday Alamba
Talla

Tun kafin ranar gudanar da zaben gwamnonin da na 'yan majalisu lamarin ke daukar hankalin mutane a ciki da  wajen Najeriya musamman a wasu jihohin kasar, cikinsu  kuwa har da Kano, da Lagos, da kuma Rivers. 

Jaridu da dama ne dai suka yi tsokaci kan zabukan na Najeriya kamar yadda suka saba a duk yayin da aka shiga muhimmin lokaci irin wannan.

The Guardian Nigeria: Babban labarin da ke shafin jaridar ‘The Guardian Nigeria’, wadda ke yanar gizo da safiyar yau shi ne, kokawar da kungiya mai zaman kanta da ke fafutukar bunkasa dimokaradiya mai suna Yiga Africa ta yi, akan rahotannin cewar, an samu yaduwar kananan makamai tsakanin mutane a Rivers, daya daga cikin jihohi 28 da zaben kujerar Gwamna da ke gudana zai fi jan hankali.

Jaridar ta ‘The Guardian’ ta ruwaito wannan kungiya ta ‘Yiga Africa’ na cewa, kananan hukumomin jihar  ta Rivers  da matsalar yaduwar kananan makaman ta fi Kamari su ne Abua-Odual, da Andoni, da Akuku Toru, da Eleme, da Gokana, Khana, da kuma Tai.

Daily Post / Daily Trust: A Legas kuwa, shugaban baki dayan tashohin mota na jihar ne Musiliu Akinsanya, wanda aka fi sani da MC Oluomo yayi amai ya ashe, kamar yadda akasarin jaridun Najeriya cikinsu har da Daily Trust da Daily Post suka ruwaito.

Lamarin dai ya samo asali ne a ranar Alhamis yayin wani taro, inda MC Oluomon ya gargadi ‘yan kabilar Igbo da ke jihar Legas da cewar, kada su kuskura su fito zabe, idan sun san ba jam’iyya mai mulki za su jefawa kuri’a ba.

Sai dai daga bisani ya fito ya bayyana gargadin da yayi a matsayin raha ce kawai ba wai barazana ba.

Idan za a iya tuna wa, a zaben shugaban kasa da aka yi a karshen watan Fabarairu, wasu ‘yan kabilar Igbo sun fuskanci barazana, inda da dama suka kauracewa wuraren kasuwancinsu a Legas, biyo bayan lashe kuri’un jihar da dan takarar jam’iyyyar Labour Peter Obi ya yi, sabanin dan takarar APC Bola Ahmad Tinubu zababben shugaban kasa a yanzu, wanda tsohon gwamnan jihar ne   

Daily Trust: Daga cikin manyan labaran Jaridar Daily Trust a shafinta na Intanet da safiyar yau akwai matakin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dauka na rattaba hannu akan wasu kudurori 16 na yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima.

Daya daga cikin kudurorin da yafi daukar hankali, shi ne wanda ya tilasta cewa daga yanzu dole ne zababben shugaba mai jiran gado ya zabi ministoci da sauran manyan kusoshin gwamnatinsa ya kuma gabatar da sunayensu ga majalisun dokokin kasar, bayan rantsuwar kama aiki a cikin kwanaki 60.

Aminiya: Ita kuwa jaridar Aminiya da ke arewacin Najeriya, cewa ta yi gwamnatin Kano ta zargi jam’iyyar NNPP ta dan takarar shugabancin kasa Rabi’u Musa Kwankwaso da shirya magudin zabe a zaben gwamna na wanan rana ta 18 ga watan Maris

Wani jami’in gwamnatin Kano ya ce Jam’iyya ta NNPP tana shirin kai masu sa ido na bogi akalla 150 domin tafka magudin zabe.

Jami’iyun biyu wato APC da NNPP sun sha zargin sunan su da yunkurin shirya magudi da haddasa fitina gabanin zaben gwamnan na yau.

Premuim Times: A na ta bangaren jaridar ta zayyana wasu jerin jihohi muhimmai da tace za a yi gumurzu sosai a yayin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi.

Daga cikin jihohin da jaridar ta bayyana da akwai

Zamfara, Lagos, Kano, Kaduna, Bauchi da kuma jihar Rivers inda tuni aka yi kira da a jibge jami’an tsaro domin yin rigakafin abinda ka iya faruwa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.