Isa ga babban shafi

Kotu ta bai wa INEC damar sake saita na'urar BVAS kafin zaben Gwamnoni

Kotun daukaka kara a Najeriya ta bai wa hukumar INEC izinin sake saita na’urar zabe ta BVAS da aka yi amfani da ita yayin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu da ya gudana a ranar 25 ga watan da ya gabata.

Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zaben Najeriya.
Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zaben Najeriya. AP
Talla

Yayin zaman kotun na yau laraba a Abuja fadar gwamnatin Najeriya, zaman da ya gudana karkashin jagorancin alkalai 3 mai shari’a Joseph Ikyegh ya karanto hukuncin kotun wanda ya sahalewa INEC saita na’urar ta BVAS gabanin zaben gwamnoni da ‘yan Majalisun jihohi da ke tafe a karshen makon nan.

Kotun ta umarci INEC ta nadi bayanan da ke cikin na’urar ta BVAS tare da adana su a waje mai tsaro baya ga sanya kwafi a rumbunan adana bayananta.  

Kafin hukuncin na yau dai, Kotu ta baiwa  dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP wato Atiku Abubakar da Peter Obi na jam’iyyar LP damar gudanar da bincike kan na’urar da sauran kayakin zabe masu muhimmanci don samun hujjojin da suke ikirarin an tafka magudi a babban zaben kasar.

‘Yan takarar jam’iyyun adawar da suka zo na biyu da na uku a zaben shugaban kasar na Najeriya wanda Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara, sun bukaci isa ga na’urorin zaben ne don tattara hujjoji bayan shigar da karar da ke kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar.

Sai dai bayan izinin isa ga na’urorin da kotun sauraren karakin zaben Najeriya ta bai wa ‘yan takarar jam’iyyun adawa, INEC ta daukaka kara kan hukuncin bisa kafa hujjoji da illar da hakan zai yi ga zaben Gwamnoni da ke tafe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.