Isa ga babban shafi

INEC ta ce babu wanda ya lashe zabe a mazabar Doguwa

Hukumar Zaben Najeriya INEC ta bayyana cewa babu wanda ya yi nasara a zaben ‘yan majalisar tarayya da aka gudanar a mazabar Doguwa da Tudunwada a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC, farfesa Mahmoud Yakubu.
Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC, farfesa Mahmoud Yakubu. © The Guardian Nigeria
Talla

Da farko dai an bayyana shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Alhassan Doguwa wanda ya tsaya takara a jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

Sai dai INEC ta cire sunansa daga cikin wadanda aka zaba kuma tare da hana shi takardar shaidar cin zabe.

Hukumar dai ta ce an tilasta wa jami’inta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hakan ya biyo bayan kame Doguwa da aka yi dangane da rikicin da ya barke a mazabar yayin da ake gudanar da zaben.

Akalla mutane biyu ne suka mutu lokacin da aka kona sakatariyar jam’iyyar NNPP a yankin.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gurfanar da babban dan majalisar a gaban wata kotun majistare wadda ta tura shi gidan yari.

Amma an bayar da belin Ado Doguwa kan Naira miliyan 500 tare da hana shi shiga lamura zaben ranar Asabar.

A ranar Laraba, Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai, babban jami’in zaben jihar, ya sanar da matakin INEC a mazabar Doguwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.