Isa ga babban shafi

INEC ta ce zabe bai kammalu ba a jihar Adamawa

Hukumar zaben Najeriya INEC, ta ayyana zaben gwamnan jihar Adamawa a matsayin wanda ba a kammala ba.

Yadda ake kirga sakamakon zabe a Najeriya.
Yadda ake kirga sakamakon zabe a Najeriya. AP - Sunday Alamba
Talla

Baturen zabe na INEC a jihar ta Adamawa, wanda ya bayyana hakan a cibiyar tattara sakamakon zabe da ke Yola, ya ce akwai bukatar sake gudanar da zabe a wasu mazabun.

Ya ce, ba za a ayyana wanda ya ci zabe ba, har sai an gudanar da zabe a wasu mazabu 47 daban-daban da ke kananan hukumomin jihar 21.

Gwamna Ahmadu Fintiri na jam'iyyar PDP na kan gaba da yawan kuri'u, inda Sanata Aisha Binani ta jam'iyya mai mulkin kasar wato APC ke biye masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.