Isa ga babban shafi

Najeriya: DSS ta ce wasu bata-gari na kitsa tashin hankali a kasar

A Najeriya hukumar tsaron cikin gida ta DSS ta ce akwai wasu bata gari da  suke kitsa tashin hankali don ganin fada ya barke a fadin kasar.

'Yan sandan Najeriya na hukumar tsaron farin kaya ta DSS.
'Yan sandan Najeriya na hukumar tsaron farin kaya ta DSS. AP - Sunday Alamba
Talla

Wannan na zuwa ne makwanni 2 bayan da hukumar ta yi  irin wannan kashedi, inda ta ke shawartar ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki su bi hanyar doka wajen neman hakkokinsu a kan abin da ya shafi zabe.

A wata sanarwar da hukumar DSS din ta fitar, kakinta, Peter Afunanya ya ce a yayin da wasu ‘yan siyasa suka kai korafe-korafensu kotu, wasu  na furta kalaman da ka iya kawo tashin hankali.

 Afunanya ya gargadi masu yada labaran karya da zummar gwara kan al’umma da  gwamnati mai ci, da su daina tun kafin rana ta baci musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.