Isa ga babban shafi

Wasu 'yan siyasa sun kuduri aniyar wargaza gwamnatin Tinubu

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya a Najeriya DSS ta bayyana cewa, akwai wasu ‘yan siyasa da ke shirya wata makarkashiya da zummar kafa gwamnatin rikon-kwarya a kasar tare da hana rantsar da zababben shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu. 

Zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu kenan daga hagu, tare da shugaba mai barin gado Muhammadu Buhari daga dama.
Zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu kenan daga hagu, tare da shugaba mai barin gado Muhammadu Buhari daga dama. via REUTERS - NIGERIA'S PRESIDENCY
Talla

Mai magana da yawun hukumar ta DSS, Dakta Peter Afunanya ya bayyana haka, yana fadin cewa, ‘yan siyasar sun nazarci hanyoyi daban-daban na ganin sun cimma burinsu, ciki kuwa har da kafa gwamnatin rikon-kwarya bayan sun yi nasarar kitsa wa kotu yanke hukuncin dakatar da rantsar da sabuwar gwamnatin kasar ta Bola Ahmed Tinubu. 

Afunanya ya ce, wadannan ‘yan siyasar na duba yiwuwar daukar nauyin wani gagarumin tashin hankali gami da zanga-zanga a manyan biranen Najeriya domin ganin an ayyana dokar-ta-baci a duk fadin kasar. 

Hukumar ta DSS ta bayyana kudirin ‘yan siyasar a matsayin muguwar aniya ta ganin cewa, an yi watsi da kundin tsarin mulkin kasar tare da yin zagon-kasa ga dokokin kasa, baya ga jefa kasar cikin mummunan rikici. 

DSS ta ce, wannan haramtaccen al’amari ba zai samu karbuwa ba a tsarin demokuradiya da kuma ga ‘yan Najeriaya masu son zaman lafiya. 

Daga karshe dai,  Hukumar Tsaron Farin Kayan ta gargadi wadanda ke shirya makarkashiyar dakile domokuradiya a kasar da su janye wannan shirin nasu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.