Isa ga babban shafi

APC, PDP sun kalubalanci DSS ta kama masu neman dakile rantsar da Asiwaju

A Najeriya, majalisun yakin neman zabe na jam’iyyar APC da na PDP sun kalubalanci  hukumar tsaro ta DSS ta yi wa wadanda suke kitsa munakisar samar da gwamnatin rikon kwarya a kasar dirar mikiya.

Zababen shugaban Najeriya, Bola Tinubu.
Zababen shugaban Najeriya, Bola Tinubu. © AP - Ben Curtis
Talla

 A mabanbantan ganawa da suka yi da wata jaridar kasar a ranare Laraba a Abuja, sun ce neman samar da gwamnatin rikon kwarya abu ne da ya saba wa doka, saboda haka kamata ya yi a kama duk Wanda yake da hannu a lamarin.

Sun bayyana haka ne biyo bayan sanarwar da huukumar tsaron DSS din ta fitar, wadda ke cewa wasu mutane na kulla munaakisar samar da gwamnatin rikon kwarya a Najeriya.

Tun da farko hukumar DSS ta fada a wata sanarwa da ta samu sa hannun kakakinta Peter Afunanya cewa wasu ‘yan siyasa a Najeriya na kokarin dakile rantsar da zababben shugaban kasar, Bola Ahmed Tinubu a ranar  29 ga watan Mayu mai zuwa.

Dan takarar APC ne dai ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu da kuri’u 8,794,726 inda ya doke abokin hamayyarsa na PDP, Atiku Abubakar, wanda ya samu  kuri’u 6,984,520 da Peter Obi  na jam’iyyar Labour mai kuri’u 6,101,533.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.