Isa ga babban shafi

Najeriya ta caccaki kasashen yammacin duniya kan tallafawa kungiyar IPOB

Gwamnatin Najeriya, ta caccaki wasu kasashen yammacin duniya kan yadda suka amince da haramtacciyar kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra IPOB, duk da kasancewar ta kungiyar ta’addanci.

Daruruwan masu fafutukar kafa kasar Biafra ne suka yi maci a titunan garin Aba da ke kudu maso gabashin Najeriya, domin yin kira da a saki jagoran su Nnamdi Kanu a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2015. Masu zanga-zangar na goyon bayan kafa kasar Biafara a yankin kudu maso gabas.
Daruruwan masu fafutukar kafa kasar Biafra ne suka yi maci a titunan garin Aba da ke kudu maso gabashin Najeriya, domin yin kira da a saki jagoran su Nnamdi Kanu a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2015. Masu zanga-zangar na goyon bayan kafa kasar Biafara a yankin kudu maso gabas. AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Ministan yada labarai da al’adu na kasar, Lai Mohammed, wanda ya yi magana a birnin Washington DC a lokacin da yake ganawa da wasu kungiyoyin yada labarai na kasa da kasa da cibiyoyin siyasa, ya ce munafunci ne kasashen yammacin duniya su yi ikrarin yaki da ta’addanci amma sai suka koma suna goyon bayan ‘yan ta’addar kungiya kamar IPOB.

Ministan ya je Washington ne don tattaunawa da kungiyoyin yada labarai na kasa da kasa da masu sanya idanu kan zaben 2023 da aka kammala.

“IPOB kungiya ce ta ‘yan ta’adda da gwamnatin Najeriya ta ayyana, amma duk da haka wasu kasashen yammacin duniya suna mu’amala da su.

"Suna ba su damar tara kudade, wasu suna ba su damar yin amfani da 'yan majalisa da kuma hadi da basu tallafi duk domin hargitsa kasar," in ji Lai.

Lai Muhammad ya kuma yi kira ga kafafen yada labarai na kasashen waje da su daina wallafa labaran ‘yan kanzon kurege na shafukan sada zumunta kan zaben Najeriya na 2023 a kan dandalinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.