Isa ga babban shafi

Za a gudanar da zabukan cike gurbi na gwamnoni da na 'yan majalisu a Najeriya

Gobe ne ake sa ran hukumar zaben Najeriya ta gudanar da zabukan cike gurbi domin tantance wadanda suka samu nasara a zaben gwamnonin Jihohin Adamawa da Kebbi da kuma majalisun tarayya a yankunan da ba’a kammala ba. 

Wata 'yar Najeriya yayin kada kuri' a zaben gwamna da na 'yan majalisu a jihar Legas.
Wata 'yar Najeriya yayin kada kuri' a zaben gwamna da na 'yan majalisu a jihar Legas. AP - Sunday Alamba
Talla

Sanarwar da hukumar zabe ta fitar a jiya, ta ce za a gudanar da zabubbukan ne a rumfunan zabe da mazabu 2,660 a kananan hukumomi 185 dake jihohi 24 a Najeriya. 

Za a gudanar da zaben gwamna a mazabu 69 dake kanana hukumomi 20 na jihar Adamawa, yayin da a jihar Kebbi za a yi zaben ne a mazabu 142. 

A bangaren majalisar dattawa kuwa, za’a gudanar da zaben cike gurbin ne a jihohin Sokoto da Kebbi da kuma Zamfara domin tantance wadanda suka samu nasara daga zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabarairu wanda bai kammala ba. 

Hukumar INEC ta ce za a gudanar da zabe a mazabu 389 da ke kananan hukumomi 23 a jihar Sokoto domin tabbatar da wadanda suka samu nasarar zuwa majalisun dattawa guda 3 da ke jihar, yayin da a jihar Zamfara za a gudanar da zabe ne a mazabu 83 da ke mazabar Zamfara ta tsakiya. 

Sanarwar ta kuma bayyana cewar za’a gudanar da zaben kujerun 'yan majalisar wakilai a jihohi 15 cikin su har da kujeru 11 da ke Sokoto da bibiyu da ke jihohin Kano da Kebbi da Oyo da Rivers da Zamfara da kuma Akwa Ibom, yayin da jihohin Anambra da Bayelsa da Edo da Imo da Kogi da Taraba da Jigawa da kuma Ebonyi ke da kujera guda-guda. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.