Isa ga babban shafi

Kudancin Najeriya bashi da kwararrun malaman da ake bukata - TRC

Hukumar dake kula da kwararrun malaman makarantu a Najeriya ta TRC tace kashi 70 na malaman dake koyarwa a makarantu masu zaman kansu a yankin kudu maso yammacin kasar basu da kwarewar da ake bukata. 

Wasu dalibai da ke karabar darasi a wata Jami'a
Wasu dalibai da ke karabar darasi a wata Jami'a © premiumtimes
Talla

Shugaban hukumar Farfesa Josiah Ajiboye ne ya gabatar da wadannan alkaluma, yayin da ya bayyana irin wadannan malamai a matsayin masu zambatar jama’a. 

Ajiboye yace irin wadannan malamai ba wai suna cutar dalibai bane kawai, har ma da bangaren koyarwa, ganin irin illar da suke yiwa harkar bada ilimi musamman ganin yadda jama’a ke biyan makudan kudade domin ganin ‘yayansu sun samu ilimin da ya dace. 

Shugaban hukumar wanda ke jawabi wajen rattaba hannu akan yarjejeniyar hadin kai tsakanin hukumarsa da Cibiyar INSTILL akan yadda za’a inganta aikin malanta a Najeriya, yace sabanin yadda jama’a ke daukar yankin kudu maso yammacin Najeriya akan ci gaban da ya samu a harkar bada ilimi, kashi 70 na wadannan malamai dake koyarwa a makarantu masu zaman kansu basu da kwarewar da ta dace su koyar. 

Ajiboye ya kuma bayyana cewar akasarin malaman dake koyarwa a Najeriya basa samu horon da ake bukata ba, yayin da kuma suke amfani da kayan aikin da aka daina amfani da su. 

Shugaban yace wadannan kalamai da yake yi sun biyo bayan binciken da suka gudanar ne a irin wadanann makarantun dake yankin da ake magana akai, abinda ya nuna cewar hukumarsa ba zata iya musu rajistar zama kwararrun malamai ba. 

Ajiboye yace suna nan suna lalubo hanyoyin da zasu bi domin cike gibin da ake da shi wajen samun kwararrun malaman da ake bukata kamar yadda kasar Afirka ta kudu tayi. 

Shugaban hukumar yace yanzu haka suna da malamai miliyan 2 da dubu 300 da suka cika sharuddan aiki a Najeriya kuma aka musu rajista kamar yadda doka ta tanada. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.