Isa ga babban shafi

Mayakan ISWAP 82 sun nutse cikin ruwa a kokarin gujewa Sojin Najeriya

Wasu rahotannin daga yankin Tafkin Chadi na cewa mayakan ISWAP da iyalansu akalla 82 sun mutu bayan nutsewa a ruwa a kokarinsu na gujewa luguden wutar sojin Najeriya yayin wani sumame da suka kai musu a jihar Borno.

Wasu mayakan Boko Haram da ke yaki da ISWAP.
Wasu mayakan Boko Haram da ke yaki da ISWAP. AFP/Archivos
Talla

Wasu bayanai da ke kunshe cikin rahoton Zagazola Makama wanda ke mayar da hankali kan al’amuran tsaro a yankin na tafkin Chadi, ya ce a mabanbantan lokuta ne iyalan ‘yan ISWAP din suka nutse a arewa maso gabashin Damasak na jihar Borno.

A cewar rahoton, yayin wani hare-haren Sojin saman Najeriya a ranar juma’ar da ta gabata ne kan maboyar mayakan na ISWAP a jihar Borno, mutanen suka sulale a kokarin tsallakawa jamhuriyyar Nijar amma kuma suka gamu da ajalinsu bayan nutsewarsu a ruwa.  

Rahoton na Zagazola Makama ya ce galibi wadanda ibtila’in ya rutsa da su mata ne da kananan yara, kuma lamarin ya faru ne a garuruwan Bulama Modori da Kaneram da Dogomolu da Jokka dukkaninsu masu gabar ruwan da ta hade da kogin Komadougou ta cikin jihar Yobe zuwa tafkin Chadi.

A wani rahoton na daban, mayakan na ISWAP sun kashe sojin Najeriya 2 cikin dakarun da aka tura Malam Fatori a karamar hukumar Abadam da ke jihar Borno ta hanyar dana abin fashewa a motarsu.

Dakarun dai wani bangare ne na Sojojin da aka aike don kara karfi ga Sojin Najeriyar da ke yaki a yanki wadanda suka farmaki mayakan na ISWAP tare da kashe mutum 3 a karshen watan da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.