Isa ga babban shafi

wata da tayi sojan gona a matsayin jami’ar kwastam din Najeriya ta shiga hanun Jami'an tsaro

Hukumar yaki da fasa kwauri wato kwastam ta Najeriya ta baiyana  cafke wata mata Rakiya Musa dake sojan gona a matsayin jami’ar ta wacce ta dade tana damfarar jama’a a kasar.

Jami'an hukumar kwastam yayin atisaye tare da sojojin Najeriya
Jami'an hukumar kwastam yayin atisaye tare da sojojin Najeriya © Daily Trust
Talla

Rakiya da a yanzu haka rumdunar ‘yansandar Najeriya shiya ta biyu dake Onikan a jihar Lagos ke bicika akan harkar ta ta sojan gona ta baiyana cewa ta dade tana mummunar sana'ar.

A yayin binciken, rakiya ta kara da cewa ta dauki shekaru 15 tana damfarar mutane kana tace akwai wani saurayin ta Akinwande Kayode da ta baiwa nera miliyan 1 daga cikin kudin da ta  damfari wasu da azal ta hau kansu.   

Da take tabbatar da kama ‘yar damfarar Sufurtendar  Hauwa Idris Adamu, jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan Najeriya shiyya ta 2, ta ce a ranar 12 ga watan Afrilun shekarar 2023 ne wasu mutane biyu Josiah Kashim Utenwojo da Dominic Okoh Henry suka mika koke ga mataimakin babban sufeton ‘yan sanda na shiyya ta 2 dake Onikan a Legas dangane da ‘Yar damfarar Rakiya Musa da ta yi ikirarin cewa ita ma’aikaciyar hukumar kwastam ce mai kula da sashin gwanjon hajoji a tashar Tin Can ta Apapa Legas.

Rakiya a kokarin ta na ganin tacimma nasara akan abin da ta sanya a gaba na cutar bayin Allah, ta zauna ne a cikin barikin sojojin jirgin saman Najeriya dake Apapa domin yaudarar wadanda take damfara saboda su tabbatar da cewa ita  jami’a ce ta hukumar ta Kwastam.

A yanzu haka dai Rakiya na hanun rundunar 'Yan sandan Najeriya don cigaba da gudanar da bincike. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.