Isa ga babban shafi

Mayakan Boko Haram sun kashe wasu manoma a jihar Borno

Mayakan Boko Haram sun kashe manoma da dama a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya. 

Wasu masu jana'izar manoman da Boko Haram ta yi wa kisan gilla a garin Zaabarmari da ke jihar Borno a Najeriya cikin shekarar 2020.
Wasu masu jana'izar manoman da Boko Haram ta yi wa kisan gilla a garin Zaabarmari da ke jihar Borno a Najeriya cikin shekarar 2020. AP - Jossy Ola
Talla

Wakilin RFI a Maiduguri, ya ce ‘yan ta’addan sun afka wa manoman ne tare da kashe su ta  hanyar fille kawunansu, yayin da suke tsaka da aiki a gonakinsu da ke yankin Molai mai nisan kilomita 5 daga babban birnin jihar ta Borno. 

Harin dai tamkar mayar da hannun agogo baya ne ga nasarorin da jami’an tsaron Najeriya suka samu kan mayakan na ‘yan ta’adda, abinda ya bayar da damar sake kankamar ayyukan noma a sassan jihar ta Borno, inda a shekarun baya hare-hare kungiyar Boko Haram ya tilasata wa dubban manoma kauracewa gonakinsu. 

Daya daga cikin ‘yan uwa ga manoman da harin ya rutsa da su, Mohammed ya ce dukkaninsu aka fille wa kawuna, a harin da ya bayyana a matsayin koma baya ga tsaro da kuma ayyukan noma. 

Mohammed ya kara da cewar suna ci gaba da neman ragowar manoman da suka ruga cikin daji domin tasrewa maharan na Boko Haram. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.