Isa ga babban shafi

Mayakan ISWAP sun kashe tarin sojojin Najeriya a wani farmaki

Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar tarin dakarun kasar yayin wani hari da 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga kungiyar IS suka kai musu a yankin tafkin Chadi.

Wasu 'yan ta'adda da suka addabi kasashen yammacin Afrika.
Wasu 'yan ta'adda da suka addabi kasashen yammacin Afrika. AFP - HO
Talla

Majiyoyi sun ce mayakan ISWAP ne suka kai wa ayarin dakarun na Najeriya hari a kauyen Metele na jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar a ranar Juma’ar da ta gabata lamarin da ya kai ga ba-ta-kashi, inda daya daga cikin ‘yan ta’addan ya tayar da damarar bam din da ke jikinsa. 

Majiyoyin sojin Najeriya sun ce an yi asarar dakarun Kasar da dama, amma ba za su iya fadin adadin wadanda suka kwanta daman ba. 

Rahotanni sun ce ayarin sojojin na kan hanyarsa ta zuwa garin Arege, wanda ke kan iyakar kasar da Nijar da Chadi don kai wa dakarun da su ke yaki da ‘yan ta’adda yankin abinci ne suka gamu da wannan harin. 

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na intanet da ake kira SITE, kungiyar ISWAP ta ce lallai ita ta kai wannan harin, kuma bam din da ya tarwatse ya lalata wasu motocin soji masu sulke guda biyu. 

ISWAP ta kuma yi ikirarin karbe dimbim makamai daga ayarin sojojin. 

Rikicin ta’addancin da ya addabi Najeriya shekaru 14 da suka wuce ya yi sanadin mutuwar kimanin mutane dubu 40, ya kuma daidaita sama da miliyan biyu, a yaayin da ya bazu zuwa makwaftanta, Nijar, Kamaru da Chadi.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.