Dakarun hadaka sun kashe 'yan ta'adda 22 a yankin tafkin Chadi
Dakarun hadaka ta kasa da kasa sun kashe kimanin mayakan Boko Haram da a kungiyar ISWAP 22 a yayin wani samame da suka kai yankin tafkin Chadi.
Wallafawa ranar:
Babban jami’in yada labaran rundunar hadakar a N’Djamena, Laftanar Kanar Kamaruddeen Adegoke ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
Kanar Adegoke ya ce an kashe ‘yan ta’addan ne a yankin karamar hukumar Abadam ta jihar Borno a ranar 27 ga watan Afrilu.
Ya ce bayan gumurzu da suka yi tare da goyon bayan rundunar sojin sama ta musamman, nazarin da suka yi ya nuna cewa an kashe sama da ‘yan ta’adda 20, aka kuma kwace bindigogi kirar AK 47 da sauran manyan makaman yaki da suka hada da motoci masu sulke.
Adegoke ya yi bayanin cewa dakarun sojin hadakan za su ci gaba da farautar ‘yan ta’adda a wani yunkuri na kara musu matsin lamba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu