Isa ga babban shafi

Sojojin Najeriya sun kashe ‘Yan ta’adda 817 da kama sama da dubu 1 cikin watanni 3

Hedikwatar Tsaron Najeriya ta ce dakarun kasar sun kashe 'yan ta'adda 817 tare da cafke masu laifi 1,326 da kuma kubutar da mutane 721 da aka yi garkuwa da su a wasu hare-hare daban-daban a fadin kasar cikin watanni uku da suka gabata.

Sojojin Najeriya a Kaduna lokacin wani rikici da 'yan Shi'a. 17/01/2013
Sojojin Najeriya a Kaduna lokacin wani rikici da 'yan Shi'a. 17/01/2013 AP
Talla

Daraktan Hulda da Kafofin Labarai na Hedikwatar Tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai ranar Alhamis a Abuja, inda ya yi karin haske dangane da ayyukan da sojoji ke gudanarwa a fadin kasar.

Buba ya ce wadanda aka kama sun hada da masu garkuwa da mutane 42, masu hada kai da ‘yan ta’adda 231 da ‘yan fashi da makami 33 da barayin shanu 80, ‘yan bindiga 325.

Sauran wadanda jami’an tsaron suka sanar da kamawa sun hada da barayin kayan jirgin kasa 27, da masu safarar makamai 73 sai kuma wadanda ake zargin barayin mai ne 191.

Arewa maso Gabashin Najeriya

Jami’in Hulda da Kafafan Yada Labaran ya kara da cewa ‘yan ta’adda 4,560 da iyalansu ne suka mika wuya ga sojoji a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya cikin watanni ukun.

Yayin da sojojin suka kwato makamai 501 da dabbobi 3,577 da alburusai iri-iri har 3,269 da sauran kayayyakin aiki 674 duk cikin wa’adin.

Manjo Janar Edward Buba ya ce, a yankin Arewa maso Gabas, dakarun Operation Hadin-kai sun kashe ‘yan ta’adda 240 inda suka kame 276 da masu hada kai da su  tare da kubutar da mutane 147 da aka yi garkuwa da su, yayin da mayaka 4,560 tare da iyalansu suka mika wuya ga sojoji.

Ya ce, sojojin sun kuma kwato makamai iri-iri 169 da alburusai iri-iri 1,195 da sauran kayan aiki 199, da suka hada da bindigogi kirar AK47 guda 57, GPMG daya, bindigar HK21 guda 2, bindigar FN daya, bindigar G3 daya da dai sauransu.

Arewa Maso Tsakiya

A yankin Arewa ta Tsakiya, Buba ya ce dakarun Operation Safe Haven sun kashe ‘yan ta’adda 94, sun kama mutane 477 da ake zargi tare da kubutar da mutane 76 da aka yi garkuwa da su, sun kuma kwato makamai iri daban-daban har 82 da alburusai 760.

Ya ce sojojin na Operation Whirl Stroke sun kashe ‘yan ta’adda 83, sun kama 104 da ake zargi, yayin da suka kubutar da mutane 18 da aka yi garkuwa da su, tare da kwato makamai 37, alburusai iri-iri 68 da kuma kayayyaki 127.

Arewa Maso Yamma

A yankin Arewa maso Yamma, Buba ya ce dakarun Operation Hadarin Daji sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda 248, sun kama 116 da ake zargin ‘yan ta’adda ne, tare da kubutar da mutane 359 da aka yi garkuwa da su, sannan sun kwato jumullar muggan makamai guda 67, alburusai 926 da sauran abubuwa 160 na munanan laifuka.

Yankin Kudancin Najeriya

A Kudu maso Kudu kuwa, ya ce sojojin Operation Delta Safe sun kashe mayakan 69, sun kama barayin mai 191 da masu hada kai da su tare da kubutar da mutane 12 da aka yi garkuwa da su.

Baba ya ce, sojojin sun kuma kama lita miliyan 6.6 na danyen mai da aka sata, lita miliyan 3.5 na Dizal da lita 188,650 na kananzir sai kuma lita 65,600 na man fetur.

Ya ce, sojojin sun kuma gano tare da lalata jiragen ruwa 249, injinan jan ruwa 28, da jiragen ruwa uku tare da kwato makamai iri-iri 51.

A yankin Kudu maso Gabas, kakakin rundunar ya ce dakarun Operation UDO KA sun kashe mayakan 80 inda suka kama wasu masu aikata laifuka da ake zargi mayakan IPOB da kawayensu na ESN 162 tare da kubutar da mutane 109 da aka yi garkuwa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.