Isa ga babban shafi

Kai hare-hare babu kakkautawa ya sanya mayakan Boko Haram mika kansu ga sojoji

Kwamandojin kungiyar Boko Haram 4 da mayakansu 13 da kuma iyayansu 45 ne, suka mika kansu da makamansu ga rundunar hadin gwiwa da ke yaki da ta’addanci ta MNJTF a kasashen da ke yankin Tafkin Chadi.

Sojojin da ke karkashin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF a yankin Tabkin Chadi.
Sojojin da ke karkashin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF a yankin Tabkin Chadi. © MNJTF
Talla

A cewar sanarwar kakakin rundunar Laftanar Kanar Abubakar Abullahi ya fitar a birnin N’Djamena na Chadi, hakan ya biyo bayan nasarar kai hare-hare da rundunar ta yi ne a ranakun 14 da kuma 15 ga wannan watan da muke ciki.

Ya ce a ranar 14 ga watan, kwamandojin Boko Haram biyu da mayakansu 9 da iyalansu 21 ne suka muka kansu da makamansu ga jami’an rundunar da ke Baga.

Haka nan a ranar 15 ga watan, kwamandoji biyu da mayakansu 4 da kuma iyalansu 24 suka mika kansu da makamai da kuma kudi ga sansanin sojojin rundunar da ke yankin Baga, a wani mataki na amsa kiran da sojojojin su ka yi wa mayakan Boko Haram na su rungumi zaman lafiya.

Sanarwar ta bukaci daukacin mayakan Boko Haram su mika kansu da kansu, domin a cewar Laftanar Kanar Abullahi, rundunar za ta ci gaba da kaiwa maboyar ‘yan Boko Haram din hare-hare babu kakkautawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.