Kano
Kotu ta mika wa Gawuna kujerar gwamnan jihar Kano
Kotun sauraren korafe-korafen zaben gwamnan Kano ta yanke hukuncin kwace nasarar da Gwamna Abba Kabir ya samu a zaben da ya gabata, inda ta bayyana Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben.
Wallafawa ranar:
Kunna - 01:34
Talla
A yayin da take yanke hukuncin, Mai Shari'a Oluyemi Akintan ta ce bisa dogaro da haramcin wasu kuri'u sama da dubu dari da sittin da biyar, ta soke nasarar ta Abba Gida Gida tare da umartar hukumar zabe wato INEC da ta mika takardun nasara ga Dakta Gawuna.
Daga Kano wakilinmu Abubakar Isa Dandago ya aiko mana da rahoto kan halin da ake ciki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu