Isa ga babban shafi

Kotu ta kori shugaban marasa rinjayen majalisar dattawan Najeriya daga kujerarsa

Kotun daukaka kara a Abuja ta soke zaben shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawan Najeriya Sanata Simon Mwadkon, inda ta bukaci sake gudanar da zabe a mazabar sa ba tare da shi ba. 

Kotun daukaka kara ta soke zaben shugaban marasa rinjaye na Majalisar dattawan Najeriya Sanata Simon Mwadkon.
Kotun daukaka kara ta soke zaben shugaban marasa rinjaye na Majalisar dattawan Najeriya Sanata Simon Mwadkon. © Aminiya
Talla

Kotun ta ce matsayin alkalan shine Jam’iyyar PDP a Jihar Filato bata bi umurnin kotu na gudanar da zaben shugabanninta a kananan hukumomi 12 kamar yadda ta bada umarni ba, saboda haka jam’iyyar ba ta da hurumin tsayar da ‘dan takara. 

Alkalan kotun sun bada umarnin gudanar da sabon zaben wanda zai wakilci mazabar Filato ta Arewa a majalisar dattawa a cikin kwanaki 90 saboda abinda suka kira kin bin umarnin kotu. 

Wannan hukunci na zuwa ne a daidai lokacin da kotunan zabe suka soke zabukan da jam’iyyar PDP ta samu nasara na kujerun majalisun tarayya a Jihar Filato, ciki harda na kujerar ‘dan majalisar dattawa da ke wakiltar Filato ta kudu, wadda tuni kotu ta mikawa ministan kwadago Simon Lalong. 

A wani labari kuma, kotun daukaka karar ta soke zaben ‘dan majalisar tarayyar jihar Filato mai wakiltar kananan hukumomin Bassa da Jos ta Arewa Musa Agah, inda ta bukaci hukumar zabe ta sake gudanar da wani sabon zabe. 

Wannan ya biyo bayan karar da jam’iyyun APC da PRP suka gabatar akan zargin tafka magudi da kuma sabawa umarnin kotu wajen gabatar da ‘dan takarar da PDP tayi a zaben da ya gabata. 

Ya zuwa yanzu jam’iyyar PDP a Jihar Filato ta rasa kujerun majalisar wakilai da na dattawa da dama a kotuna saboda kin bin umarnin kotu na sake gudanar da zaben shugabanninta na kananan hukumomi 12. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.