Isa ga babban shafi

Yau kotun daukaka kara ke fara sauraron shari'ar zaben gwamnan jahar Kano

A yau ne kotun daukaka kara ta jahar Kano da ke Arewacin Najeriya, za ta fara sauraron karar da gwamnan Jahar Abba Kabir Yusuf ya shigar, don kalubalantar hukuncin kotun sauraron korafe-korafen zaben Jahar da ya soke zabensa.

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf © Abba Kabir Yusuf
Talla

A ranar 20 ga watan Satumbar daya gaba ne dai kotun sauraron zaben jahar Kano, ta soke zaben dan takarar Jam’iyar NNPP Abba Kabir Yusuf, tare bayyana dan takarar Jam’iyar APC Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben.

Kotun dai ta soke kuri’un Abba Yusuf dubu dari da 65 da dari 663, inda ta kafa hujja da cewa babu sahannun hukumar zaben kasar INEC a jikinsu.

A ranar 18 ga watan Maris din wannan shekarar ne hukumar INEC ta sanar da gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jahar, bayan da ya samu kuri’u miliyan daya da dubu 19 da dari 602, yayin da Nasiru Gawuna ya samu kuri’u dubu dari 890 da dari 705.

Toh sai dai bayan da kotun sauraron korafe-korafen zaben gwamnan ta soke kuri’a dubu 165 da dari 663 na Abba Yusuf, Gawuna ya shiga gabansa da sama da kuri’u dubu 30.

Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC da kotun sauraron kararrakin zaben Kano ta mika wa kujerar gwamnan Jihar, bayan kwacewa daga Abba Kabir Yusuf na NNPP.
Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC da kotun sauraron kararrakin zaben Kano ta mika wa kujerar gwamnan Jihar, bayan kwacewa daga Abba Kabir Yusuf na NNPP. © Daily Trust

Kotun ta kuma bayyana Gawuna a matsayin wanda yayi nasarar lashe zaben, sannan ta bukaci hukumar INEC ta janye takardar shedar zaben Abba Yusuf da mikawa Gawuna.

Rashin amincewa da wancan hukuncin ne dai ya sanya Abba Yusuf da jam’iyarsa ta NNPP da kuma INEC suka garzaya kotun daukaka kara don kalubalantarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.