Isa ga babban shafi
Zaben jihar Kogi

Sayen kuri'a ya mamaye zaben jihar Kogi duk da baza jami'an EFCC da ICPC

Sayen kuri’u sun mamaye wasu rumfunan zabe a zaben gwamna da ke gudana a jihar Kogi. Rahotanni sun ce da yawa daga cikin masu kada kuri’a na tattaunawa kan yadda aka yi musu alkawarin basu naira dubu 5 kan zabin wata jam’iyya.

Wani rumfar zabe yayin zaben gwamna da majalisun jiha a Najeriya. 18 ga watan Maris 2023
Wani rumfar zabe yayin zaben gwamna da majalisun jiha a Najeriya. 18 ga watan Maris 2023 AP - Sunday Alamba
Talla

Hakan na faruwa ne duk da baza jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifuka ICPC a jihar domin tunkarar matsalolin sayen kuri’u.

Jaridar Daily Trust ta ce wakilinta ya ci karo da irin wannan al’amari a rumfar zabe da ke Miami da ke kusa da yankin Adankolo na jihar inda wakilin wata jam’iyya ke sanya ido sosai domin tabbatar da cewar an dangwala jam’iyyarsa tare da nuna masa a fili kafin biyan kudi.

Haka lamarin ya ke a unguwar Angwa Pawa da ke Lokoja, inda aka gayyaci galibi masu kada kuri’u mata zuwa wani lungu, aka ba su wani adadi tun kafin su je kada kuri’a.

Wani mai lura da zaben da ya badda kama ya tabbatar da cewa daya daga cikin wakilan wata jam’iyya ya tuntube shi domin ya zabi jam’iyyarsa tare da yi masa alkawarin cewa za a ba shi naira 5,000, sun dauka mai kada kuri’a ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.