Isa ga babban shafi

Gobara ta lashe wani sashe na kasuwar Gamboru dake Maiduguri

Najeriya – Wata gobara ta lakume wani sashe na kasuwar Gamboru dake birnin Maiduguri a Najeriya, abinda ya haifar da asarar dukiya mai tarin yawa.

Wannan hoton wata Gobara ce a wata kasuwa
Wannan hoton wata Gobara ce a wata kasuwa AFP
Talla

Rahotanni daga Maiduguri sun ce gobarar ta tashi ne tun daren jiya asabar, kuma tayi ta ci har zuwa yau da safe ba tare da anyi nasarar kashe ta ba.

Wannan iftila’in na zuwa ne watanni 5 bayan gobarar ta lashe wani sashe na kasuwar a watan Maris na wannan shekarar, abinda ya sanya ‘yan kasuwa da dama tafka asara.

Ya zuwa wannan lokaci ba’a iya tantance abinda ya haddasa gobarar ba, yayin da aka sanar da cewar ma’aikatan kashe gobara sun kwashe sa’oi suna kokarin ganin bayan ta.

A bara ne aka samu irin wannan gobara a Monday market, kasuwa mafi girma a birnin Maiduguri, wadda ta haifar da mummunar asarar dukiyoyi da kuma katse harkokin kasuwanci.

Tuni gwamnatin jihar ta sake gina kasuwar da kuma sake mika ta ga ‘yan kasuwa domin ci gaba da harkokin su na yau da kullum.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.