Isa ga babban shafi

Rahoto kan yadda kogin matan fada a Argungu ke barazanar kafewa

Gulbin Matan Fada, wuri ne da ake gudanar da bikin kamun kifi na kasa da kasa a garin Argungu da ke jihar Kebbin tarayyar Najeriya, to sai dai yanzu haka wannan kogi na fuskantar barazana sakamakon yadda ruwan da ke shayar da shi ke sauya wa kansu hanya daga ƙaramar hukumar Augie da ke jihar, kuma tuni wannan matsala ta tada hankalin wasu Kabawa da ba su zaci faruwar hakan ba.  

Kogin Matan Fada a Argungu, wajen da ya shahara don gudanar da bikin kamun kifi na kasa da ke gudana duk shekara a jihar Kebbi ta Najeriya.
Kogin Matan Fada a Argungu, wajen da ya shahara don gudanar da bikin kamun kifi na kasa da ke gudana duk shekara a jihar Kebbi ta Najeriya. © Daily Trust
Talla

Yanzu haka dai gwamnatin jihar Kebbi na duba yadda za ta bullo wa wannan matsalar kamin lokacin da aka saba gudanar da bikin kamun kifi duk da cewa ba a kai ga sanya ma sa lokaci ba.  

Faruk Muhammad Yabo, ya kai ziyara a garin na Argungu ga kuma tsarabar da ya zo mana da ita.  

Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.