Isa ga babban shafi

Tinubu ya dakatar N-Power da shirin ciyar da daliban firamare a sassan Najeriya

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi umarnin dakatar da ilahirin shirrye-shiryen tallafawa marasa karfi da ke karkashin kulawar hukumar ayyukan jinkai ta kasar, matakin da ke zuwa bayan zargin badakalar rashawar da ta dabaibaye ma'aikatar.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. 09/10/23
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. 09/10/23 © Bola Ahmed Tinubu twitter
Talla

Wata sanarwa da Ofishin sakataren gwamnatin Najeriya ta fitar a yammacin yau juma'a mai dauke da sa hannun kakakin ofishin Segun Imohiosen ta ce shugaba Tinubu ya yi umarnin dakatar da shirye-shiryen nan take.

A cewar sanarwar shirye-shiryen da dakatarwar ta shafa sun kunshi N-Power da Conditional Cash Transfer sai shirin bayar da jari da kuma ciyar da daliban Firamare da gwamnatin Najeriyar ta shafe shekaru ta na yi a sassan kasar.

Kamar yadda sanarwar ta ambata, dakatarwar za ta kasance ta wucin gadi zuwa nan da makwanni 6 don gudanar da bincike a hukumar dangane da badakar rashawar da ta dabaibayeta, gabanin duba yiwuwar dawo da su ko muma maye gurbinsu da wasu.

A baya-bayan nan ne dai shugaban Najeriyar Bola Tinubu ya dakatar da ministar ayyukan jinkai Betta Edu kan badakalar Naira miliyan 585 wadda tuni ta fara fuskantar tuhuma daga hukumar EFCC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.