Isa ga babban shafi

An gano gawarwakin mutane 5 cikin guda 100 da kwale-kwale ya kife da su a Neja

Ana fargabar kifewar wani makeken kwale-kwale ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a jihar Neja da ke tsakiyar kasar.

Har yanzu gawarwakin mutane 5 ne kadai aka gano
Har yanzu gawarwakin mutane 5 ne kadai aka gano AFP / JOHN WESSELS
Talla

Bayanai sun ce kwale-kwalen na dauke da mutane fiye da 100, zuwa yanzu an gano gawarwakin mutane biyar cikin 100 da da suka nitse a ruwan.

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar ta bakin Darakta Janar dinta Alhaji Abdullahi Baba-Arah, ta ce ta sami rahoton kifewar kwale-kwalen a karamar hukumar Borgu

Sanarwar da Baba-Arah ya fitar ta ce kwale-kwalen makare da mutane da kayan su ya tashi ne daga Kauyen Dugga Mashaya kuma ya dau hanyar zuwa kasuwar Wara da ke jihar Kebbi.

Har kawo wannan lokaci dai babu wani bayani a hukumance kan dalilin kifewar jirgin, said ai Darakta Baba- Arah ya ce akwai alamu lodin da ya wuce kima ne ya haddasa hadarin.

Hadarin kwale-kwale ba sabon abu bane a Najeriya musamman daga bara zuwa bana inda akalla hadurra mabanbanta suka kashe dubban mutane a sassan kasar daban-daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.