Isa ga babban shafi

Najeriya za ta fara amfani da kudaden tallafin yaki da HIV, TB da Malaria

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da shirin fara aiwatar da tallafin dala miliyan 933 da asusun duniya ya bai wa kasar domin yaki da cutukan kanjamau, tarin fuka da zazzabin cizon sauro tsakanin shekarar 2024 zuwa 2026.

Najeriya na sahun kasashen da ke matukar amfana da tallafin Asusun Duniya wajen yaki da cutukan 3.
Najeriya na sahun kasashen da ke matukar amfana da tallafin Asusun Duniya wajen yaki da cutukan 3. Solacebase
Talla

A jawabinsa gaban taron aza harsashin fara amfani da kudaden da ya gudana a Abuja fadar gwamnatin Najeriyar a jiya Talata Farfesa Muhammad Ali Pate da zai ja ragamar shirin a wani yunkuri na rage ta’azzarar cutukan 3, ya ce baya tallafin magungunan cutukan shirin zai kuma taimaka wajen samar da sabbin tsare-tsare a fannin lafiyar da nufin bunkasawa ko kuma karfafa sashen lafiyar kasar.

Farfesa Pate ya bayyana cewa Najeriya ce kasa mafi karbar kaso mai yaw ana tallafin asusun duniyar daga 2021 zuwa 2023 da ya kunshi dala biliyan 1 da miliyan  200 na yaki da cutar Covid-19.

A cewar Farfesa Pate gogewar da bangaren lafiyar Najeriya ke da shi ta fannin gwaje-gwaje da bincike dama hanyoyin tunkarar cutuka zai taimaka matuka wajen fasalta yadda za a yi amfani da shirin yaki da cutakan 3 na HIV Aids da tarin fuka da kuma zazzabin cizon sauro a tsawon lokacin na 2024 zuwa 2026 karkashin tallafin.

Farfesa Muhammad Pate ya ce zuwa karshen karshen shekarar 2023 alkaluma sun nuna yadda aka gudanar da gwaje-gwajen cutukan fiye da miliyan 87 cikin shekaru 5 a sassan Najeriya wadanda suka gudana da taimakon asusun na Duniya, wanda ke matukar taimakawa a yaki da cutukan musamman HIV Aids.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.