Isa ga babban shafi

Sumaila yaki amincewa da sauke daraktan NNPC da Tinubu ya yi

Najeriya – ‘Dan Majalisar dattawan Najeriya daga Jihar Kano, Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila yaki amincewa da bukatar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na maye gurbin Babban daraktan dake kula da wani sashe na kamfanin man kasarna NNPC dake kula da bangaren gas, Mansur Kuliya daga jiharsa domin maye gurbinsa da Oluwole Adamu.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu © premiumtimes
Talla

Sumaila yace rashin adalci ne matakin da shugaban kasar ya dauka na tube Kuliya daga mukaminsa na shekaru 5, kasa da shekaru 2 da nada shi a kan mukamin, domin maye gurbin sa da wani.

A wasikar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rubutawa shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, ya bukaci majalisar da ta amince da nadin Adamu, inda nan take Akpabio ya mikawa kwamitin dake kula da bangaren gas da man fetur domin ya fara aikin tantance sabon daraktan.

Sumaila yace sabuwar dokar man fetur da majalisar tai ta bayyana yadda ake nadi da kuma tube shugabannin bangarorin man fetur, saboda haka ganin Mansur Kuliya da ya fito daga mazabarsa ya fara wannan aikin ne a watan Maris na shekarar 2022, kuma ba’a same shi da karya wata doka ba, babu hurumin tube shi daga mukaminsa.

‘Dan majalisar ya bukaci Majalisar dattawa ta mutunta dokokin da tayi da kanta wajen kaucewa karya doka ko kuma ci gaba da tantance Adamu ba tare da wasu hujjojin da dokar tayi tanadi a kai ba.

Yayin mahawara a zauren majalisar, shugaban ta Akpabio ya bukaci ‘yan kwamitin tantancewar da su yi la’akari da korafin da sanata Kawu Sumaila ya gabatar da kuma dokar da suke aiki da ita.

‘Yan Najeriya sun dade suna korafi a kan yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke tube manyan ma’aikata daga mukaman su ba tare da aikata wani laifi ba, tana maye gurbin su da wasu, duk da yake dokar dake kula da ma’aikatun su ta bayyana karara wa’adin nadin da ake musu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.