Isa ga babban shafi

Bankin Duniya zai bai wa Ghana bashin dala miliyan 300

Bankin Duniya ya amince da bai wa Ghana bashin dala miliyan 300, domin taimaka wa kasar wajen farfado da tattalin arzikinta da ya shafe shekaru yana fuskantar koma baya.

Kasuwar kayayyakin abinci ta Agbogboloshie da ke Accra, babban birnin kasar Ghana.
Kasuwar kayayyakin abinci ta Agbogboloshie da ke Accra, babban birnin kasar Ghana. ASSOCIATED PRESS - OLIVIER ASSELIN
Talla

Cikin sanarwar da ya fitar, Bankin Duniyar ya ce zai mika wa Ghana tallafin bashin ne daga asusunsa na IDA da ke tallafa wa kasashe masu fama da talauci.

A makon da ya gabata ne dai, kasar ta Ghana ta samu nasarar karbar kashin farko na jimillar bashin dala biliyan 3 daga assusun ba da lamuni na duniya IMF, wanda ya fara mika mata dala miliyan 600 daga ciki.

A cikin watan Oktoban shekarar bara ta 2023, Bankin Duniya ya sanar da cewar kashi daya bisa 4 na 'yan kasar Ghana na fama da talauci ganin yadda suke rayuwa a kan kasa da dala 2 a kowacce rana. 

A dai farkon watan na Oktoban barar ne kuma, dubban mutane suka fito kan tituna a Accra babban birnin Ghana, suna neman a tsige gwamnan babban bankin kasar bayan zarginsa da gazawa wajen tafiyar da harkokin tattalin arzikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.