Isa ga babban shafi

Najeriya ta sake karya darajar naira karo na biyu cikin watanni 8

Najeriya ta rage darajar kudin kasar, wato Naira a karo na biyu cikin watanni 8, a kokarin da ta ke na kawo sauyi a kasuwar musayar kudaden waje tare da jan hankalin masu zuba jari don ceto tattalin arzikinta daga rugujewa.

Kudin naaira na Najeriya..
Kudin naaira na Najeriya.. © Bashir Ahmad
Talla

Darajar naira ta yi mummunar faduwa a wannan mako bayan da mahukunta a babban bankin kasa suka yi wasu gyare-gyare a kan yadda ake lissafin farashinta, lamarin da ya daga farashin dala a hukumance zuwa kusan yadda take a kasuwannin bayan fage.

 

Masana da dama na daukar wannan lamari a matsayin gyare-gyaren da ake yi don jan hankalin ‘yan kasuwa, wadanda shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya hau karagar mulki a watan Mayun shekarar da ta gabata ya bijiro da su.

 

Biyo bayan gyare gyaren da aka yi  a kan tsarin da ake lissafin farashin naira, yanzu babban bankin kasar ya fara wallafa farashin kudaden musayar a shafinsa na intaenet, inda a hukumance ake sayen dalar Amurka a kan  naira dubu 1 da dari 357.

 

A farkon wannan  makon, sai da babban bankin ya kai caccaki ‘yan canji da abokan huldarsu, wadanda ta ce su na kawo bayanan karya a kan farashin da naira, lamarin da ke kawo sabani a kasuwar hukuma.

 

Rage darajar  naira da babban bankin Najeriya ta yi ya kara nauyn basukan da kamfanin jiragen saman kasashe waje da ke aiki a kasar ke bin hukumomi.

 

Aa ranar talatar da ta gabata, babban bankin Najeriya ya ce ya biya kamfanonin jiragen sama da ke aiki a kasar dukkan kudaden dalar da suke bi,  bayan da ya biya karin dala  miliyan 64.

 

Amma kungiyar  mau sufurin jiragen sama ta kasa-da-kasa ta ce tana maraba da biyan da babban bankin ya yi, amma har yanzu kamfanonin sufurin jiragen saman a bin gwamnatin kasar  bashin dala miliyan dari 7.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.