Isa ga babban shafi
FADUWAR DARAJAR NAIRA

Babban bankin Najeriya na zargin bankuna da sayar da dala ta bayan fage

Najeriya – Babban bankin Najeriya na CBN ya sanar da tura jami’ansa masu sanya ido a bankunan kasuwanci saboda zargin da ake musu na boye takardun dalar Amurka da yawansu ya kai dala biliyan 5 da kuma taimakawa wajen faduwar darajar naira. 

Hedikwatar babban bankin Najeriya CBN da ke birnin Abuja.
Hedikwatar babban bankin Najeriya CBN da ke birnin Abuja. REUTERS - AFOLABI SOTUNDE
Talla

Babban bankin na CBN ya dora alhakin wahalar da aka shiga na tsadar farashin kudaden kasashen waje da kuma faduwar darajar naira a kan yadda bankuna ke sayar da su ta bayan fage ga ‘yan canji wadanda ke haifar da karancin su ga 'yan kasuwa da kuma mabukata a cikin Najeriya.

Wannan zargi ya bullo ne sakamakon yadda  babban bankin ya nuna damuwarsa kan yadda ake fuskantar matsalar samun kudin a bankunan kasuwancin, yayin da kuma alkaluman dake gaban sa ke nuna irin yawan dalolin da bankunan suka mallaka a fadin kasar.

A ranar alhamis dai kasuwar canjin kudin ta rufe ne ana sayar da farashin dalar Amurka a kan naira dubu 1 da dari 450 a kasuwannin canji na bayan fage.

Domin nuna muhimmanci a kan matakan da babban bankin ya dauka dangane da wannan matsala ta karancin dalar da kuma tashin farashinta, babban bankin ya dauki matakin tura  jami’ai da zasu sanya ido tare da binciken musabbabin wannan matsalar.

Bankin na CBN ya daura damarar  shawo kan matsalar ta tashin farashin dalar da kuma faduwar darajar naira da take zargin bankuna da haddasawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.