Isa ga babban shafi

INEC na gudanar da zabukan cike gurbi a jihohi 26 na fadin Najeriya

Najeriya – Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa a Najeriya na gudanar da zabukan cike gurbi da sake gudanar da wasu zabuka a jihohi 26 dake fadin kasar a yau Asabar.

Tambarin dake nuni da yadda za a kada kuri'a
Tambarin dake nuni da yadda za a kada kuri'a Yasuyoshi CHIBA / AFP
Talla

Hukumar tace ana gudanar da zaben ne a kananan hukumomi 80 dake fadin yankunan da ke da rajista 575 da kuma rumfunan zabe 8,934.

Jihohin 26 sun hada da Ebonyi, Yobe, Kebbi, Lagos, Ondo, Taraba, Benue, Borno, Kaduna, Plateau, Akwa Ibom, Anambra, Cross River, Delta, Enugu, Jigawa, Katsina, Adamawa, Bauchi, Bayelsa, Kano, Nasarawa. Niger, Oyo, Sokoto and Zamfara.

Shugaban hukumar zaben ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa masu kada kuri’a miliyan 4 da dubu 904 da 627 ne suka yi rajista kafin zabe, yayin da  katin zabe na dindindin miliyan 4 da dubu 613 da 291 aka karba.

Ana gudanar da zabukan cike gurbi na ‘yan majalisar dattawa guda biyu, na ‘yan majalisar wakilai hudu da na majalisun jihohi uku a jihohi tara sakamakon mace-mace da aka samu da kuma sauka daga kujera bisa ra’ayi ko wasu dalilai.

Haka kuma an sake gudanar da zaben wanda ya biyo bayan umarnin kotu a majalisar dattawa daya da mazabu 11 na tarayya da kuma na jiha 22.

Daga cikin zabukan da za a gudanar akwai na wadanda za su maye gurbin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Bola Tinubu, Femi Gbajabiamila, Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, Ministan Ayyuka, David Umahi, Ministan harkokin 'yan sanda, Ibrahim Geidam, da karamin ministan ilimi, Tanko Sununu, wadanda duk suka yi suka ajiye kujerunsu don karbar mukamai a gwamnatin shugaba Tinubu.

Haka kuma, ana gudanar da zabukan cike gurbi na maye gurbin Isma’ila Maihanchi, zababben dan majalisar wakilai daga jihar Taraba da ya rasu gabanin kaddamar da majalisar dokokin kasar da kuma Abdulkadir Danbuga daga jihar Sokoto wanda ya rasu a watan Oktoban 2023.

Daraktar hulda da jama'a ta hukumar, Zainab Aminu Abubakar tace sun dauki duk matakan da suka dace wajen ganin an gudanar da sahihin zabe a wadannan mazabu.

Abubakat ta shaidawa RFI Hausa cewar tuni a rarraba kayan aiki da kuma jami'an gudanar da zaben domin kaucewa samun matsala, yayin da ta ce umarnin kotu ya hana sanya jam'iyyar PDP a zaben jihar Filato.

A ranar Alhamis ne babban Sifeto Janar na ‘yan sandan kasar, Olukayode Egbetokun, ya bayar da umarnin hana duk wani nau’in zirga-zirgar ababen hawa a kan tituna, hanyoyin ruwa, sararin samaniya, da sauran hanyoyin sufuri daga karfe 12 na safe zuwa 6 na yamma a dukkanin jihohin kasar 26 gabanin zaben da za a yi ranar Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.